Saturday, 18 August 2018

Yadda wasu matasa su 8 suka yi ma wata Akuya fyade yayin da take dauke da ciki



Rundunar Yansandan kasar India sun kaddamar da farautar wasu matasa su takwas da ake zargi da zakke ma wata Akuya mai dauke da juna biyu, ta hanyar yi mata fyade, wanda hakan yayi sanadin mutuwar Akuyar, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar Arewarmu.com ta ruwaito ana tuhumar matansan ne a karkashin sashi na 377 na kundin hukunta manyan laifuk, wanda ya haramta auren jinsi, ko kuma saduwa ba kamar yada ake yi bisa al’ada ba.

Bugu da kari yansanda na tuhumar matasan da cin zarafin dabba, wanda hakan yi ma dokar hana cin zarafin dabba karan tsaye ne.

“kakakin 'yan sandan yace Mun gano guda uku daga cikinsu, kuma jami’an Yansandanmu suna farautarsu ruwa a jallo, muna sa ran zamu kama su nan bada jimawaba.” Inji kaakakin Yansandan yankin, Naazneen Bhasin.

Bhasin yace mai Akuyar ne ya kama uku daga cikin matasan turmi da tabarya yayin da suke yi ma Akuyar fyade da tsakar dare a satin daya gabata, ya kara da cewa bayan wani dan kankanin lokaci ne kuma Akuyar ta mutu.




SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: