Wednesday, 5 September 2018

Ladan noma: Wani manomi ya dauki alwashin saya ma Buhari takardar takara

Wani manomi da cikin manoman da suka amfana da tsare tsare harkar noma da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bullo dasu ya bayyana bukatarsa ta yankan ma shugaban kasa Muhammadu Buhari takardar tsayawa takara na jam’iyyar APC.

Mun ruwaito Kaakakin jam’iyyar APC reshen jahar Legas, Joe Igbokwe ne ya sanar da haka a shafinsa, inda ya bayyana sunan wannan manomi a matsayin Kabiru Ishaq Sa’idu.

Malam Kabiru yace: “A matsayina na manomi, kuma wanda ya kirkiri kungiyar manoman ‘Northern Avengers’ zai taimaka ma bukatar shugaban kasa na sake komawa kujerarsa a karo na biyu, don haka zan bada naira miliyan 5, taimakona don sayan takardar takararsa.

“Zan yi haka ne don nuna godiyata ga Baba Buhari, bisa kokarin na baiwa manoma kwarin gwiwa, tare da nuna ma yan Najeriya cewa harkar noma itace hanyar samun arziki cikin sauki, tare da zama da kafarka.” Inji Kabiru.

Malam Kabiru ya kirkiri Northern Avengers ne don mayar da martani da tsagerun Neja Delta da suka kafa wata kungiya mai suna Niger Delta Avengers, suna fasa bututun mai, suna kashe jami’an tsaro tare da garkuwa da mutane.

A wani labarin kuma, jam’iyyar APC ta fitar da sahihin farashin shiga takara a karkashin inuwarta, inda ta sanya naira miliyan 40 ga masu sha’awar takarar shugaban kasa, da miliyan 20 ga masu takarar gwamna.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: