Monday, 24 September 2018

Manyan Dalilan Dake Sa Mata Sanya Make-Up A Wannan Zamani

Mata da dama basu iya fita sai da ado, domin suna tunanin wannan adon ya kan kawo masu farin jini tare da koma bayan haka.

Mafi yawancin mutane sukan yi tambayar, me ke sa mata yawan sanya make-up?

Ga amsar wannan tamabayar kamar yadda wasu matan suka shaida mana nan kasa:

1. Sanya make-up na taimakawa wajen boye kama ko kawar da kurajen fuska


Mafi yawanci babban dalilin dake sanya suna saka make-up shine domin boye kama. Mata na ikirari cewa wasu mazzan na ganin munin su idan basu sanya make-up ba.

2. Yana karfafa takama da nuna izza


Akwai takama da izza dake tare da mace wanda tayi ado kuma ta sanya kayan make-up. Idan ka gan mai haka to ka san cewa ta cika yar kwalisa.

3. Wasu na sanyawa don kawai suna son yin haka


Kamar yanda maza ke son sanya manyan riguna hakazalika mafi yawanci mata ke son sanya make-up.

4. Domin jawo hankalin jama’a da nuna kyau


Babu tantama idan mace ta sanya make-up ta kan jawo hankalin jama’a dake kusa da ita kuma yana sanya mutane suyi mata shaidar kyakyawa.

5. Idan bata sanya ba a tunanin ta adon ta bai cika ba


Ga wasu abun ya bi jiki domin suna ganin idan basu sanya ba tamkar kamar basu yi ado ban sha’awa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: