Tuesday, 25 September 2018

Siyasar Kano Ga dalilin da yasa Kwankwaso ya tsayar da surukinsa takarar gwamnan kano



Yayin da ya gana da manema labarai a garin Kano ranar Litinin 24 ga wata, Rabiu Musa Kwankwaso, yace surukinsa ba mijin hajiya bane domin yana da mata biyu.

Rabiu Kwankwaso  (Daily Post)
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana dalilin da yasa ya tsayar da surukinsa takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam'iyar PDP.
Kwankwaso wanda ke neman kujerar shugaban kasa ya tsayar da mijin diyar shi, Abba Kabir Yusuf, a matsayin wanda zai daga tutar PDP a zaben 2019 sabanin yadda jama'a suka yi tunani duba da irin goyon bayan da tsohon matimakin gwamnan jihar na yanzu da kuma Takai wanda ya fito takarar kujerar a zaben 2015.

Da yake zantawa da manema Labarai yayin da ya kai ziyara Kano ranar Litinin 24 ga wata, Kwankwaso yayi ikirari cewa surukin tasa ba mijin-hajiya bane domin yana da mata biyu kuma yadda matar sa zata juya shi.

A labarin da Daily Nigerian ta fitar, tsohon gwamnan yace masu korafi game da takarar wanda ya tsayar su mayar da hankalin su wajen gani ko ya cancanta.

Kwankwaso ya ce bayan nazari da tuntuba da shawara da suka yi da mutane da dama tsawon shekara uku da doriya domin duba wanda ya kamata su tsayar a takara ba tare da an sake maimaita abin da ya faru ba na sabani da matsalolin da suka samu kansu a ciki, kuma yawanci suka nuna cewa Abba K. Yusuf ne ya fi dacewa.

Sanatan ya ce wanda suka yanke shawarar tsayarwar wanda shi ne kwamishinan ayyuka a lokacin gwamnatinsa ta wa'adi na biyu, shi ne ya jagoranci dukkanin ayyukan cigaba da aka yi a jihar a lokacin.

Ya ce yana bakin ciki da watsi da gwamnatin jihar ta yanzu tayi da ayyukan da gwamnatina tayi, amma Abba ya fi shi bakin ciki a kai, don haka yana ganin idan har ya samu hawa kujerar gwamnan za a raya wadannan ayyuka, a kuma dora a kai.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: