Tuesday, 25 September 2018

Ahmed Musa ya samu kyautar gwarzon watan Agusta a Saudi Arab



Gabanin wasan firemiya na kasar wanda kungiyar sa ta buga da  tawagar Al-Taawoun ranar Litinin 24 ga wata aka mika masa kyautar.

Ahmed Musa  (Al Nassr)
Dukanin alamu na nuna cewa Ahmed Musa ya shiga kasar Saudiya da kafar dama, ya lashe kyautar gwarzon dan wasa na watan farko na gasar firemiya na kasar.
Gabanin wasan firemiya na kasar wanda kungiyar sa ta buga da  tawagar Al-Taawoun  ranar Litinin 24 ga wata aka mika masa kyautar.

Tauraron dan wasan tawagar Super Eagles  na cigaba da haskawa bayan komawar sa kungiyar Al-nassr daga Leicester na Ingila.

Wasan sa na farko a kungiyar, Ahmed Musa ya zura kwallo a raga a wasan su da Al-jazira  wanda aka tashi 2-1, Al-nassr ta samu galaba.

Kungiyar sa ta samu nasara a wasan inda ta doke abokin adawar da kwallo daya babu ko daya.

Dan wasan yana daya daga cikin fitattun yan wasa dake taka leda a kasar kana ya samu kyakkyawar tarba daga masoya a kasar.

Ahmed Musa ya samu wannan kyautar mako daya bayan da ya taimaki kungiyar sa da kwallo uku a ragar abokan adawar su.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: