Babbar magana : Aisha Buhari Uwargidan shugaban kasa na zargin dogarin ta da karban kudi da sunanta
Ana dai zargin CSP Sani Baban Inna da karbo kudaden da yawansu ya kai Naira biliyan biyu da rabi daga wasu jami'an gwamnati da abokan arzikin uwar dakinsa da sunan tallafi zuwa gareta.
Aisha Buhari (Punch)
Tun a ranar Jumu'ar da ta gabata ne dai bayanai suka ce an kama dogarin na uwargidan Shugaban kasa Aisha Buhari, a yayin wani samame da 'yan sanda suka kai gidansa bayan da ta yi zargin cewa ya zambace ta zunzurutun kudi har Naira biliyan biyu da miliyan 500.
Ana dai zargin CSP Sani Baban Inna da karbo kudaden da yawansu ya kai Naira biliyan N2.5b daga wasu jami'an gwamnati da abokan arzikin uwar dakinsa da sunan tallafi zuwa gareta.
Sai dai dangin jami'in dan sandan sun musanta wannan zargin kana bayanan binciken da aka yi a gidan nasa da kuma a asusun ajiyarsa na banki ya nuna babu alamun makudan kudi irin haka a cikinsu.
Amma kuma sakamakon binciken bai kwantawa uwar dakin tasa rai ba ganin cewa 'yan uwansa 'yan sanda ne suka yi binciken.
Uwargidan shugaban kasa Buhari ta mika maganar ga hannun hukumar 'yan sandan ciki wato SSS wadda ke ci gaba da binciken wannan maganar kawo yanzu.
Tace bata taba tura dogarinta wajen karban kyuata a madadin ta.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun uwargidan shugaban kasa, Suleiman Haruna, ya fitar, tayi kira ga duk wanda yayi mu'amala da dagari da suyi gaggawa wajen kai kara domin a mayar da kudaden da suka rasa.
A sanarwar tana mai cewa "Kamar yadda kowa ya sani, jami'in 'yan sanda ne, kuma hukumar 'yan sanda ce da kanta ta kama shi domin ta bincike shi a kan wasu zarge-zarge da aka yi masa cewa ya je ya karbi kudade da sunanta, da sunan 'ya'yanta cewa suna neman kudi"
A halin yanzu CSP Sani Baban-Inna na tsare yana fuskantar bincike kan wannan zargin da uwargidan shugaban kasar ke yi masa.
0 comments: