Thursday, 27 September 2018

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama wani mutumi da ya hargitsa tsarin zabe a Osun


- Jami'an rundunar yan sandan Najeriya sun kama wani mutumi da ake ganin yana hargitsa tsarin zabe da ake sake gudanarwa a Osun

- An kama mutumin ne a mazaba ta 5, Ataoje E a Osogbo

- Kimanin mutane 884 aka yiwa rijista a wannan mazabar

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa jami'an rundunar yan sandan Najeriya sun kama wani mutumi da ake ganin yana hargitsa tsarin zabe a wani mazaba a Osogbo, babban birnin jihar Osun.

A cewar Channels TV an kama mutumin ne a mazaba ta 5, Ataoje E a Osogbo wacce ta yi rijistar masu zabe 884.


Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama wani mutumi da ya hargitsa tsarin zabe a Osun
A halin da ake ciki unguwuar Idiya, Ward 8, Unit 1, karamar hukumar Orolu, wasu yan baranda sun fitittiki jama'a da suka fito kada kuri'a da safen nan. yanzu haka mutanen sun nemi mafaka a fadar Olufon of Ifon-orulu.

Bayan wannan hari da aka kai Orolu, mazauna garin Disu sunce sun fasa kada kuri'a sakamakon cin mutuncin da akayi musu jiya. Sun bayyana cewa an hanasu fitowa daga gidajensu.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: