Sunday, 30 September 2018

Musha Dariya: Datijjo Kafi Kukan Aski

Wani sarki ne ana yi masa aski, to wanzamin irin masu zafin hannu ne, in suna maka aski kaji kamar za su cire maka fatar kai..
To wanzami fa ya kama kan sarki yana ta gurza, sarki kuma azaba ta ishe shi ya rasa yadda zai yi, kar yayi magana yaji kunya, za'a ce sarki na kukan aski..

Sai aka yi sa'a Can cikin gida sai wani dan akuya ya dinga kuka ''6eee! 6eeee!! 6eeee!!!

Sai sarki ya daga murya yace sarkin cikin gida?? Sai ya amsa na'am ranka ya dade'' sai sarki yace duba ka gani wai dan akuyan nan ko shi ma askin ake yi masa ne??

Sarkin gida ya gane nufin sarki yace ''kai dan talakawa saki kan sarki ka bar gidan nan''

Dattijo kafi kukan aski......

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: