Monday, 1 October 2018

Najeriya ta cika shekaru 58 da samun yancin kai: Jerin shuwagabanninta tun daga 1960



A yau 1 ga watan Oktobar shekarar 2018 ne kasar Najeriya ta cika shekaru hamsin da takwas (58) da samun yancin kai daga hannun yan mulkin mallakar kasar Birtaniya da suka kwashe sama da shekaru dari suna bautar da Najeriya.

Tun bayan samun mulki daga kasar Birtaniya, Najeriya samu shuwagannin kasa goma sha shidda, sai dai wasu daga cikinsu sun maimaita ne har sau biyu, wannan yasa NAIJ.com ta yi kokarin tunatar da masu karatu shuwagabannin da Najeriya ta yi har zuwa yanzu.

1 Abubakar Tafawa Balewa 1960-1963
2 Nnamdi Azikiwe 1963-1966
3 Manjo Janar Johnson Aguiyi-Ironsi 1966
4 Janar Yakubu Gowon 1966-1975
5 Janar Murtala Mohammed 1975-1976
6 Manjo Janar Olusegun Obasanjo 1976-1979
7 Alhaji Shehu Shagari 1979-1983
8 Manjo Janar Muhammadu Buhari 1983-1985
9 Janar Ibrahim Babangida 1985-1993
10 CifErnest Shonekan 1993
11 General Sani Abacha 1993-1998
12 Janar Abdulsalami Abubakar 1998-1999
13 Cif Olusegun Obasanjo 1999-2007
14 Alhaji Umaru Musa Yar'Adua 2007-2010
15 Dakta Goodluck Jonathan 2010-2015
16 Malam Muhammadu Buhari 2015

Haka zalika bayan samun yanci, watau a jamhuriya ta daya an samu shuwagabannn shiyyoyin Najeriya huda uku da suka hada da shiyyar Arewa, shiyyar kudu da kuma shiyyar yammacin Najeriya, wadanda suka samu shwuagabanni kamar haka.

Shiyyar Arewa Ahmadu Belli Sardauna daga 1 oktoba 1960 – 15 Janairu 1966
Shiyyar kudu Michael Okpara daga Oktobar 1960 - Janairun 1966
Shiyyar yamma Samuel Akintola daga oktobar 1960 – Janairu
n 1966

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: