Saturday, 22 September 2018

Rahama Sadau Dakatarwa da aka yi mun ya bude mun kofofin samun nasara


Rahama tace mutane da dama da basu santa a da suna goyon bayan ta yanzu

Rahama Sadau
Shaharariya ‘yar wasan kwaikwayo Rahama Sadau ta bayyana cewa korar da ƙungiyar MOPPAN na masana'antar Kannywood tayi mata ya bude mata kofofin samun nasara tare da karin masoya.

Fittaciyar jarumar ta ayana haka a wata hira ta musamman da tayi da jaridar Guardian lifestyle.

“Ina mai godiya game da haka don ya bude mun kofofin nasara a masana’antar fina-finai. a da Mutane da dama basu san dani ba sai da aka kore ni, ba abun alfahari bane amma ina ganin kaddara ce daga Allah” inji rahama.

Game da dalilin da yasa aka kore ta tauraruwan tace;

“ dan kawai na taba mutum aka kore ni. Lamarin addini da Imani tsakanin mutum ne da ubangijin sa. na taso a matsayin ‘yar arewa , na san iyakoki na kuma na san abubbuwan da ya kamata inyi ko in hana a matsayi na ‘yar arewa kuma musulma”.

Rahama tace hakika ba ko wani matsayi da aka bata tayi take karba indai matsayin ya saɓawa addinin ko al’adar ta.

Haifiyar jihar Kaduna ta kara da cewa ta watsi da wani matsayyi da aka bata na kwaikwayan yan madigo don ya saɓawa addinin ta.

Kusan shekara daya kenan da ta samun korar daga masana’antar Kannywood bayan ta rungumi mawaki Classiq a cikin wani bidiyon wakar shi.

Yar wasan ƙwaikwayon tace wannan ya bude mata kofofin samun nasara tunda yanzu har ta fara fitowa a shirin fina-finan masana’antar Nollywood da dama tare da wasu nasarori.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: