- A kauyen Nahuce, karamar hukumar Bungudu ne aka sace su
- Yan bindigar sun ce sai an basu Naira miliyan 100
Jami'an 'yan sanda a jihar Zamfara dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga da basu san ko suwa ne ba sun sace wani dan siyasa da kuma wasu mutane shida a kauyen Nahuce dake a karamar hukumar Bungudu.
Yan sandan dai sun ce dan siyasar da aka sace tare da sauran mutanen shine Bello Dan Iya dake zaman tsohon Kansila na mazabar ta Nahuce da sanyin safiyar ranar Lahadi.
Kuma wani da lamarin ya auku akan idon sa mai suna Malam Sani Ibrahim ya shaidawa majiyar mu cewa 'yan bindigar sun shigo ne da nufin sace shugaban karamar hukumar Bungudu Alhaji Hamisu amma sai basu samu nasara ba.
Haka zalika kamar yadda muka samu, 'yan bindigar tuni sun yo waya inda suka bukaci iyalan wadanda suka sace din da su tattara masu Naira miliyan 100 kafin su sako su.
A wani labarin kuma, Yanzu haka an fara dar-dar a tsakanin 'yan Najeriya bayan da kungiyoyin ma'aikatan dake hada-hadar kasuwannin mai a Najeriya suka sanar da kudurin su na shiga yajin aiki na sai-baba-ta-gani.
Kamar yadda muka samu, kungiyoyin ma'aikatan man dai sunce za su shiga yajin aikin ne bisa dalilin muzgunawa da wasu daga cikin mambobin su ke fuskanta da wasu kamfunnan kasashen waje.
0 comments: