Saturday, 22 September 2018

Yadda Adam Zango ya jawo ni na shiga harkar waka – Aliyu Sharba

Mawaki Aliyu Sharba na daya daga cikin matasan mawakan Hausa masu tasowa, ya yi wa Aminiya bayani kan yadda ya shiga harkar da alakarsa da Adam S. Zango da kuma dalilinsa na hada waka da kasuwanci:


Mene ne tarihinka a takaice?
Sunana Aliyu Usman, sai dai an fi sanina da Aliyu Sharba. Ni dan asalin garin Buni-Yadi ne da ke karamar Hukumar Gujuba a Jihar Yobe. A can na yi makarantar firamare da sakandare. Bayan nan na dawo nan Abuja na fara harkar kasuwanci, sai kuma waka da nake yi a yanzu.

Wace harkar kasuwanci ka fara kafin waka?
Har yau har gobe ina gudanar da kasuwanci, ina harkar sayar da man dizel (man gas) kamar yadda aka fi saninsa a Arewa. Nakan kai wa kamfanoni da sauransu. Wannan na taimaka min kwarai wajen sama min abin yi. Idan ban samu aikin waka ba, sai na samu a harkar kasuwar. Ke nan ya zame min tamkar garkuwa. Saboda idan ka ce aikin wakar kadai za ka rike ba tare da wata sana’a ba, to wani zubin sai a samu bacin rana, abubuwa su cije. Amma idan kana da abin yi sai ka ga an fita kunya.

Me ya ja ra’ayinka ka shiga harkar waka?
Maigidana Adam Zango na daya daga cikin wadanda na ga ayyukansu sannan na kwadaitu da wannan harka ba don komai ba, sai saboda nishadantarwa da burgewa da ayyukansa suke yi duk lokacin da ya tsara waka. Kuma adalilin yadda nake bibiyansa sau-da-kafa, a wasu lokutan idan na fitar da waka sai a dauka ko nasa ne.

Zuwa yanzu wadanne bangarori ne wakarka ta fi karkata?

Ta shafi bangarori da yawa, ta hada da wakokin soyayya da na bikin aure da kuma siyasa, duk wanda ta kama ina yi. Sai dai na fi ba da muhimmanci a wakoki na albam nawa da nake yi sai kuma na fim.
A cikin wakoki da ka yi wacce ce za ka ce ta fi fitar da kai a wajen jama’a?
A gaskiya suna da yawa, sai dai muhimmai a ciki, su ne kamar wakar da na yi mai suna “An tashi” da kuma “Mamarki da Mamata kawaye ne,” sai kuma “’Yar Kaduna” sai dai idan za a ce na fitar da guda a ciki, to ba kamar wannar waka mai suna “Da mamarki da Mamata kawaye ne.” Waka ce da ta bayyana yadda soyayya ta shiga tsakanin saurayi da budurwa wadanda iyayensu mata kawayen juna ne kuma na yi ta ce a kan abin da ya faru da ni kaina da wata ’yar kawar Mamata a can gida. Sai dai afuwan ba zan iya ambata maka sunanta ba (dariya).

Wadanne irin sakonni ne wakokinka ke dauke da su?
Yawanci wakokina sun kunshi fadakarwa ce ga jama’a a kan wasu abubuwa da watakila ba su mayar da hankali a kai ba, ta hanyar nishadantarwa. Misali guda da zan ba ka shi ne sakon da ke cikin wakata da na yi mai suna “An tashi.” Waka ce da za a iya gabatar da ita a wajen biki na aure da sauran bukukuwa. Tana kunshe da abubuwa da ke bayani a kan sha’anin rayuwa na yau da kullum.

Kana da takamaiman inda kake gudanar da ayyukan wakokinka?
Ina da sutudiyo nawa da ke garin Lugbe, Abuja kuma a nan nake gudanar da wakokina. Wani zubin kuma nakan yi tattaki zuwa wajen mai gidana Adam Zango a Kaduna ko kuma abokan aikina Kano, to nakan yi wasu ayyukan a can. Ziyarata wajen Adam Zango ta kunshi abubuwa biyu ne, zan samu zarafin yin aiki a karkashinsa kuma zan koyi darasi. Wani zubin shi ne ke gayyatata idan wani aiki ya taso da yake ganin zan dace da shi wani zubin kuma ni nake zuwa.

Kamar abokan aiki nawa kake gudanar da ayyuka da su a wajen naka?
Ba za su gaza 20 ba, wannan ya hada maza da mata. Sai dai fa ba wai adadin baki dayan wadanda ke zuwa wajen nan ke nan ba, domin akwai masu zuwa jifa-jifa. Ina yi maka bayani ne a kan wadanda muke gudanar da ayyuka tare da su wadanda wasu sa’annina ne wadansu kuma yarana. Mukan shirya albam na bidiyo tare da su.


Wane irin alheri za ka ce ka samu?
A gaskiya na samu alheri da yawa a cikin shekara wajen 10 da nake wannan sana’a. Na farko dai a ciki na bude wannan sutudiyo da nake aiki, na yi gida na yi mota. Koda yake sana’ata ta farko ta taimaka min. To da abin da nake samu a nan din da na wancan idan aka hada sai ka ga abin ya bada ma’ana an yi wani abin arziki da shi.


Yaya batun iyali kuma?

Batun iyali sai dai niyya. Ina nan ina kokari tare da sa ran in Allah Ya yarda nan da wani lokaci ai dai a samu labari mun shiga sahu.
A duk wani abu da mutum ke yi bai ratsa wani kalubale, kai a naka wane iri ka fuskanta?
Ba a rasa kalubale kamar yadda ka bayyana, sai dai da farko zan gode wa iyayena, ban samu wata matsala ta bangarensu ba a lokacin da na bayyana musu kudirina na shiga cikin wannan harka ta waka, saboda baki dayansu sun ba da goyon baya tare da sa albarka, watakila wannan shi ne babban dalilin da ya sa ban fuskanci matsala ba. Matsala guda da nake fuskanta ita ce ta wajen da muke yin wasa wato lokeshin, inda a wani lokaci sai a samu akasi a kan wajen daukar shirin (shooting), wani karon sai mun tuntubi mahukunta wurin amma lokacin da aka je da jama’a tare da kayan aiki don dauka, sai su bukaci a dage saboda rana ce ta aiki da makamantan haka. Wani zubin kuma jami’an tsaro ne za su zo idan suka tarar kuna aiki, sai su ce ba su amince a haska wurin ba. To irin wadannan abubuwa sukan jawo mana asara, sai ka ga duk abubuwa da aka tanada don su dace da yanayin wurin sun tafi a banza.
A karshe wane buri kake da shi a wannan sana’a taka?
Burina shi ne kamar yadda na yi bayani a baya wato in ga na kasance daya daga cikin jaruman fina-finan Hausa, da kuma faranta wa masoyana rai a cikin duk abin da na yi, sannan na zama sanadiyyar zaburar da wadansu zuwa ga aikin kyautata wa al’umma. Wadannan su ne muhimman buri da nake da su.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: