Jarumin barkwanci a masana’antar Kannywood kuma mawaki da tauraronsa ke cigaba da haskawa Ado gwanja ya samu karbuwa a zukatan masoya masu bibiyan fina-finan hausa.
Haka zalika yana da farin jini a fagen waka musamman daga mata duba da irin wakokin biki da yake rairawa. Bisa ga wannan dalilin aka yi masa lakabi da ‘limamin Mata’.
Mawakin yana daya daga cikin fitattun yayyan kamfanin White house Family wanda Adam A.Zango ke jagoranta. Zango maigidansa ne hakazalika shima mawakin baya boye ma jama’a dangatakar dake tsakaninsu.
Mun kawo maku wasu abubuwa biyar da muke son ku gane dangane da jarumin kamar haka;
1. Shi ruwa biyu ne
Duk da cewa shi dan asalin jihar Kano ne, Mahaifinsa dan garin Warawa ne dake Kano kuma mahaifiyar sa yar kabilar shuwa Arab ce daga jihar Borno.
2. Karatun sa
Ado Gwanja ya yi karatun firamarensa a makarantar Babbangi dake Karkasara. Sannan ya yi karatun sakandare a Sakandiren kofar Nasarawa. Bai samu ya cigaba da karatunsa bayan Sakandare. Bayan rasuwar mahaifinsa jarumin ya shiga buga-bugar rayuwa har Allah Ya kawo shi zuwa ga matsayin da yake yanzu.
3. Harkar waka ya fara
Yawanci ana ganin cewa jarumin ya fara da harkar sai dai a yadda ya bayyana, ya fara aiki a masana’antar nishadi ta fagen waka. Yace sama da shekaru 12 yake waka sai dai kuma a wancan lokacin ba’asan shi kana bai samu kudin shiga situduyo ba don buga waka.
4. Wanene gwaninsa
Hakika dangantakar shi da sauran mawaka mai kyau ce kuma akwai girmamawa tsakanin, mawakin yace babban gwanin sa a wannan harkar shine mawaki Aminu Maidawayya.
5. Dalilin da yasa ya fiye yin wakar mata
Sanin kowa ne cewa hazikin mawakin ya fiye yin wakokin biki wanda ana iya cewa wakokin mata ne sai dai mafi yawanci ba’a san dalilin da yasa ya shahara a wannan fagen ba wanda yasa ma har ake kiran sa da ‘limamin mata’. A cewar shi dalilin da yasa yake yin wakokin biki.

0 comments: