Mene ne muhimmancin motsa jiki? Kuma wane lokaci ya dace ayi shi?
-N.I, Ringim.
Ba shakka motsa jiki akai-akai na daya daga cikin hanyoyin samun koshin lafiya. Bincike dabam-dabam ya nuna cewa motsa jiki kan hana cututtuka irin na zuciya da na mutuwar barin jiki aukuwa, ta hanyar kona man cholesterol, da rage hawan jini, da rage siga a jiki ga masu ciwon siga da ma wadanda basu da ciwon. Wato dai a hannu daya motsa jiki riga-kafi ne babba daga ciwon siga, ciwon zuciya, ciwon hawan jini, ciwon mutuwar barin jiki, wasu ciwukan na daji wato kansa, ciwon baya, ciwon jiki, ciwon damuwa na depression, ko na kasala da ma wasu da dama. A daya hannun kuma motsa jiki kan yi maganin duk wadannan ciwuka idan basu yi nisa sosai ba.
Binciken suka kuma ci gaba da nuna cewa mai motsa jiki akai-akai bayan annashuwa da zai rika ji a ransa, da kuma jin karfin jiki ta hanyar kara kwarin kasha, ana sa ran kuma zai samu karin shekaru a duniya.
A mafi yawan lokuta mutane sun fi jin dadin motsa jiki da safe, amma masana sun tabbatar da cewa ko da wane lokaci ma ana iya yi don za a iya samun duk fa’idojin da ake samu da safen. Ba wai kawai ka zage da tikar gudu a fili shine kawai motsa jiki ba, a’a idan ka yi tafiyar minti 45 a kowacce rana ko da mintina 15 sau uku (wato ya dai tashi minti 45) indai za ka yi a kullum, to kana daya daga cikin mutane masu motsa jiki.
Wane irin abinci ya kamata a ba yaro dan wata shida?
-Habibu, Gusau.
Daga wata shida bayan ruwan nono, akan iya fara ba yaro ruwa mai tsabta (tunda da munce ba a ba jariri ruwa har tsawon wata biyar ko shida sai ruwan nono kacal). Wannan ne zai kare shi daga kamuwa da kwayoyin cuta masu sa zawo. A wannan wata ne kuma ake so a fara sabawa yara da abinci mai dan ruwa-ruwa, wato kamu mai madara da ayaba, ko kunun gyada, ko cerelac, ko frisocrem daidai karfin mutum. Haka har wata tara inda za a kara da irinsu dafaffen kwai, indomie, taliya, da sauran abinci maras nauyi kamar ‘ya’yan itatuwa.
Ina tambaya ne akan lemon tsami, don an ce yana da illa. Kuma idan ba illa ana iya sha a shayi? Kuma da gaske yana da sinadaran rage kitse?
–Khadija, Hotoro.
A dan binciken da na gudanar ban gano inda aka fadi illar lemon tsami ba indai shansa za a yi ba sawa a wani wuri ba. Wurin da aka ce yana wa illa kawai shine hakora saboda sinadarin acid din citric acid. Wato idan ana yawan shansa zalla ba a abinci ba na tsawon shekaru, zai iya kashe hakora.Amma amfaninsa yafi illar yawa. Don haka idan aka sashi a abinci ko shayi kamar yadda kika fada, zai iya rage karfin acid din. Bayan acid akwai sinadarai da dama irinsu vitamin kala-kala a cikinsa masu kara lafiya, da sinadaran anti-oxidants masu kona kitsen jiki.
Idan mace ta samu ciki a mara yake zama koda yaushe? Kuma wane wata yake fara motsi?
-Safiya, Samarun Zariya
Mahaifa dai a mara take. Kashi 98 cikin dari na ciki na zama a mahaifa. A ragowar kashi 2 ciki zai iya zama ko ina a wajen mahaifa ko a mara, bayan mahaifar ko a gefe, ko kuma a ciki kusa da hanji. Shekaru biyu da suka wuce a kasar Birtaniya da kuma Australia an yi wa wasu mata tiyata a ciki an fidda ‘ya’ya ‘yan watanni tara da suka rayu a ciki kusa da hanji ba a mahaifa ba. A mafi yawan lokuta dai, wannan ciki kan zama hadari ga lafiyar uwar. Akan iya kiyaye irin wannan idan ana zuwa awo.
Jariri a mahaifa kan iya fara motsi lokacin da aka busa masa rai tun daga misalin wata na hudu ko kwanaki 120.

0 comments: