Saturday, 22 September 2018

Yadda Ake Hada Kunun Kwakwa Mai Gwanin Dadi

Kamar yadda akwai nau’o’in kunu kamar; kunun gyada, kunun tsamiya, kunun aya da sauransu. Haka kuma akwai kunun kwakwa wanda ba ko wacce mace ne ta son da shi ba. An fi son a yi wannan kunu ne domin tarbar baki ko don karyawa a gida.


Abubuwan da za a bukata

Kwakwa

Danyar shinkafar tuwo

Madara

Sukari

Citta

Injin din markade (blender).

Hadi
Za a wanke danyar shinkafa kamar wankin gero, sai a sanya mata citta kadan ba mai yawa ba. Sannan a kai injin markade a nika kullun. Bayan haka, sai a yi tata kamar dai yadda ake tace kamu. A jira ya kwanta. A samu kwakwa a kankare bayanta mai launin ruwan kasa har sai ta yi fari tas. Sannan a yanka ta kanana yadda za ta iya nikuwa a injin markade. Idan ta yi laushi sai a samu tukunya a tace a ciki. Sannan a dora ruwan kwakwar a kan wuta. Idan ta tafasa, sai a dama kullun danyar shinkafar nan daidai misali a zuba sai a cigaba da gaurayawa har sai ya yi kauri, sannan a sauke. Idan ya dan huce sai a zuba madarar gari da sukari daidai dandano, kafin a fara sha. Himmmn! Wannan kunun ba a bai wa mai kiwuyaa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: