Ana tuhumar limaman coci da lalata yara a church
Ma'aikatar shari'a a Amurka ta bude bincike akan zargin cin zarafin yara ta hanyar lalata da ake yi wa daruruwan limaman cocin Roman Katolika.
Babban lauyan gwamnatin Jihar Pennsylvania ya aikewa akalla limamai 4 takardar neman su bayyana a kotu.
Masu gabatar da kara sun bukaci wasu takardun sirri da shaidu daga jami'an kotun.
A bangarenta cocin ta fitar da wata sanarwa inda ta tabbatar da cewa an aika musu da takardar neman bayyana a gaban kotu.
Sanarwar ta ce za ta bayar da cikakken hadin kai kan bukatar, kamar yadda ta bayar da hadin kai.
A watan Agusta wani rahotan tawagar lauyoyi ya gano sahihan shaidu da ke nuna cewa sama da yara dubu daya ne limaman coci 300 suka ci zarafinsu a fadin jihar ta Pennsylvania kuma jami'an kotu na rufa-rufa a kai.
0 comments: