Fallasa: An gano wasu makuden biliyoyin daloli da aka sace daga NNPC a zamanin Jonathan
An gano cewar an sace danyen mai wanda kudinsa ya kai $12.7 bn daga Najeriya zuwa kasashen waje daga 2011 - 2014
- Babban lauya, Femi Falana ne ya bayyana hakan a taron murnar cika shekaru 40 da kafa kungiyar manyan ma'aikatan man fetur da iskar gas
- Falana ya yi kira ga gwamnati, kungiyar dillalan man fetur da sauran masu ruwa da tsaki su taimaka domin ganin an karbo wadannan kudaden
A jiya Alhamis ne fitaccen lauya mai kare hakkin bil adama a Najeriya, Femi Falana (SAN) ya yi ikirarin cewar an sace danyen mai wanda kudin shi ya kai $12.7 biliyan a Najeriya daga shekarar 2011 zuwa 2014.
A jawabin da ya yi wajen bukin murnar cika shekaru 40 da kafa kungiyar manyan ma'aikatan fanin fetur na iskan gas na Najeriya a Abuja, Falana ya bukaci a fara gudanar da bincike nan take domin gano inda kudaden suka makalle tun 2014.
Ya kuma yi kira ga kungiyar dilalan man fetur na kasa PENGASSAN ta su taimaka wa hukumomin yaki da rashawa domin tabbatar da cewar an gano inda kudaden suke tare da hukunta wadanda ke da hannu cikin karkatar da kudin.
Babban lauyan ya ce ya samu wannan alkalluman ne daga wata bincike da Nigeria Maritime Administration and Safety Agency ta fitar kuma ya yi alkawarin bawa hukumar NNPC da sauran masu ruwa da tsaki rahoton domin suyi nazari.
"Binciken ya nuna cewar an sace danyen mai daga Najeriya wanda kudinsa ya kai $12.7 biliyan. An sauke danyen man a wani tashan jiragen ruwa kuma mun gano kamfanoni da 'yan kasuwar da ke da hannu kuma tun 2014 muke rokon gwamnati ta dauki mataki, " inji Falana.
A jawabinsa, babban Manajan NNPC, Maikanti Baru ya yi kira ga PENGASSAN ta bawa hukumar hadin kai domin ganin an warware matsalar.
0 comments: