MAGANIN BASUR DA KAIKAYIN MATSE-MATSI :
Assalamu Alaikum, Dan Allah Mal. Ataimaka Min Da Maganin Rashin Rike Alwala, Dadewar Matse-Matsi, Rashin Digewar Fitsari Da Kuma Kankancewar Gaba. Nagode!!!!
AMSA
*******
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Wadannan larurorin kusan tushensu guda ne. Ga wata fa'idah nan ka jarraba :
- Sassaken Qirya, Sassaken dinya, sassaken tsada, ganyen saiwar sabara.
Ka hadasu waje guda ka dakasu ka nikesu, Sannan ka rika diban cokali guda na garin maganin kana jikawa kana sha.
Sannan ka samu man lalle kana shafawa amatse-matsin naka kullum kafin ka kwanta barci.
In shaAllah zaka samu lafiya daga matsalolin basur, rana, kankancewar gaba, dadewar matsematsi, etc.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU (09/02/1440 18/10/2018).
0 comments: