Jarumin ya shiga harkar fina-finai ne a dalilin kai sakon sarkoki da mahaifinsa ya aike shi ya kai wa V. Shantaram.
Anan ne ya samu aka saka shi a cikin wani fim mai suna Navrang a shekarar 1959.
Da ya ke mai sha'awar fina-finan kasarsu ne, ya yi rawar gani a cikin wannan fim din.
Sakamakon yadda ya taka rawa a wannan fim, sai ya burge mutane da dama, hakan yasa masu shirya fina-finai suka fara rububin sanya shi a cikin fim dinsu.
Fim din Jeetandra na farko da ya yi fice sosai shi ne Geet Gaya Pattharon Ne wanda aka yi a 1964.
Fim dinsa na Farz, shi ne ya kara haskaka tauraruwarsa.
Rawar da Jeetandra ke yi a cikin fina-finansa, musamman rawa irin ta zamani wato (Disco), ita ta kara masa farin jini a wajen ma'abota kallon fina-finan Indiya musamman matasa a wancan lokaci.
Mutane da dama na sara masa saboda rawa a cikin fim, kuma ba rawar disco kadai ba, har ma irin ta su ta gargajiya kowacce in dai za a ce masa ga yadda ake so ya yi, to ko zai yi ita.
Da wa yafi fitowa a fim
A kalla Jeetandra ya fito a fina-finai kusan 200, ba na Hindu kawai ba, har da na Telugu.
Kuma a mafi yawan fina-finansa na Hindu tun da sun fi yawa, ya fi fitowa da marigayiya Sridevi da kuma Jaya Prada.
Amma kuma ya yi fina-finai masu dan dama da Reena Roy da Neetu Singh da kuma Hema Malini.
Su waye iyalan Jeetandra?
Jeetandra ya kasance daga cikin wadanda suka nemi Hema Malini da aure, amma kuma abin bai yi wu ba, don haka sai ya koma ya fara neman Shobha Kapoor.
Shobha Kapoor ta kasance ma'aikaciyar jirgin sama a kamfanin jiragen sama na British Airways a wancan lokaci.
A shekarar 1974 ne suka yanke shawarar yin aure, kuma suka yi aure wanda ba a yi wani shagali ba don ba a gayyaci mutane sosai ba.
Wadanda suka kasance a wajen auren sun hadar da iyalan ma'auratan da kuma abokan Jeetandra wato Rajesh Khanna da kuma Sanjeev Kumar.
Har yanzu suna tare da matarsa inda suka samu 'ya'ya biyu, wato Ekta Kapoor da Tushar Kapoor.
Ekta ita ce shugabar kamfanin shirya fina-finai na babanta wato Balaji Telefilms, yayin da shi kuma Tushar jarumi ne wanda ya gaji mahaifinsa.
Lambobin yabon da ya karba
Jeetandra ya samu lambobin yabo sakamakon rawar da ya taka a fina-finai.
Ya samu lambobin yabo da dama da suka hada:
1998 - Guest of Honour Award at the 18th Ujala Cinema Express Awards[9]
2000 - Lifetime Achievement Award in film personalities[10]
2002 - Lifetime Achievement Award at the Zee Gold Bollywood Movie Awards in New York.[11]
2003 - Filmfare Lifetime Achievement Award
2004 - "Legend of Indian Cinema" Award at Atlantic City (United States).[12]
2005 - Screen Lifetime Achievement Award
2007 - Dadasaheb Phalke Academy Award[13]
2008 - Sansui Television Lifetime Achievement Award[14]
2012 - Zee Cine Award for Lifetime Achievement
2012 - Lions Gold Awards: Most Evergreen Romantic Hero
Wasu daga cikin fina-finansa sun hadar da:
Caravan
Himmatwala
Jaani Dushman
Tohfa
Nagin
Judaai
Sindor
Hoshiyaar
Jaani Dost
Mawaali
Justice Chaudhury
Suhaagan
Aulad
0 comments: