Wani bincike ya gano cewa akwai kimanin mutum miliyan 200 ke fama da cutar zazzabin cizon sauro a fadin duniya, adadin ya hada da mutane 584, 000 da ke mutuwa a kowacce shekara, wadanda mafi yawan su kananan yara ne, yan kasa ga shekara biyar, a yankin saharar Afirka. Binciken ya kara da cewa, masana sun tabbatar da cewa cutar tana yaduwa ga jama’a ta hanyar cizon harbabbiyar ta-macen sauro (Anopheles).
Lokaci ya yi da za a hada hannu wuri guda domin yaki da wannan hatsabibiyar cuta ta maleriya, tare da rage karfin ta. Dakta Bolajoko Olusanya, babban daraktan cibiyar ‘Healthy Star Initiatibe, Global Burden of Disease Collaborator’, ya ce cutar zazzabin cizon sauro ita ce cuta kwaya daya wadda ke sahun gaba tare da jawo mutuwar jama’a a wajen kisan jama’ar da suka doshi 192, 284 a Nijeriya. Bugu da kari kuma, ya ce alamu sun nuna kan cewa maleriya cuta ce mai kisa wadda kuma matukar ba a dauki kwakkwaran matakin magani a kan kari ba, ta na jawo mutuwa. Sannan kuma, daukar matakin dakile yaduwar sauron tare da cizon, shi ne kawai babbar hanyar kare kai daga cutar maleriya.
Amfani/kwanciya a gidan-sauro: Kwanciya a cikin gidan-sauro yana daya daga cikin muhimman kare kai daga cizon sauro, kuda da sauran kwari masu lahani ga rayuwar dan Adam. Wannan shi ne babban matakin da zai hana sauro ya samu kafar yada cutar maleriya, ta hanyar cizon. Kuma ya kamata a lizimci kwanciya a cikin gidan-sairon, a kowanne lokaci; sannan a rinka kula dangane da wani sa’in sauron ya na yin sanda ya shiga cikin gidan-sauron ba a sani ba- domin kare kai.
Yin feshin maganin kwari a kai a kai: Magungunan feshi wadanda aka yi su domin kashe kwari. Ana bukatar yawaita amfani da kalar magungunan feshen, ta ingantaciyar hanya, wadanda zasu taimaka wajen kashe kwarin (sauro) domin dakile yaduwar su tare da jawo lahani ga jama’a. Bugu da kari kuma, dole a kula da karkashin gado, kan kowacce kwana a cikin dakin ko wasu lunguna wadanda sauron ke makalewa a ciki. Har wa yau, a bayan fesa maganin kashe kwarin, kar a manta da cewa ana bukatar mutum ya fita daga cikin dakin, da zarar ya fesa maganin.
Amfani da gogon tufafi, domin kare kai daga cizon sauron: A hannu guda kuma, masana sun bayar da shawara kan cewa, daya daga cikin hanyar kare kai daga kamuwa daga cutar cizon sauro, akwai amfani da dogon tufafi wadanda zasu rufe jiki domin rage yawan cizon sauron. Musamman yadda muhallin mu yake fama da shara tare da nau’ukan kazanta da suke taimaka wa sauro hayayyafa. Bisa ga wannan ne, ya kamata a kula tare da tsaftace muhalli, kamar yadda ya kamata, saboda sauro yana kyankyashe ‘yayan sa ne ta hanyar kwantaccen ruwa da ake bari a gidajen mu, ko kusa damu.
Hanyoyin karfafa garkuwar jikin mutum: Dangane da ha kan ne masana ke baiwa jama’a shawara wajen amfani da nau’ukan abinci masu gina jiki tare da karfafa garkuwar jikin dan Adam, domin samun sukunin juriya tare da yakar wasu cutuka a jikin shi.
Yawan amfani da magungunan rage karfin cutar maleriya; a kai a kai: A karshe, daya daga cikin hanyar rage karfin kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro tare da yakar ta, masana sun bayar da shawara kan cewa mutane su rinka amfani da magungunan yaki da cutar maleriya, ta hanyar shawarar kwararrun likitoci- lokaci bayan lokaci.
Har wa yau, ana amfani da wadannan magungunan ne ta hanyar kwararrun likitoci ko likitocin kimiyyar harhada magunguna. A nemi shawarar kwararrun likitoci a duk lokacin da mutum ya tabbatar da kamuwa da cutar zazzabin cizon sauron, a kan kari- kana da taka-tsantsan dangane da lamarin a kowanne lokaci.

0 comments: