Tuesday, 16 October 2018

Kai Duniya!!! Miji Ya Kama Matarsa Da Tohon Mijinta A Gidansa Suna Lalata

A yau Litinin ne wata kotun Majistare da ke zamanta a Mapo da ke Ibadan ta raba datse igiyar aure tsakanin Barakat Adeniyi da Abdulrazak Adeniyi bisa zargin cin amanar aure da rashin kulawa da hakkin aure.

Shugaban kotun, Alhaji Suleiman Apanpa ya bayyana cewar kotun ta raba auren ne saboda dukkan ma'auratan biyu sun nuna cewar ba su sha'awar cigaba da zama da juna.

A karar da Barakat ta shigar da farko, ta zargi mijinta da nuna halin ko in kula gare ta da dan ta inda ta ce ya kwashe makonni biyu bai duba lafiyarta ba ko na dan su.


A bangarensa, Abdulrazak wadda malamin Islamiyya ne ya karyata zargin da matarsa ke masa inda ya ce ba ta da da'a har ma yana zarginta da bin wasu mazaje.

"Baraka ta dena shayar da yaron mu nono watanni biyar bayan haihuwa ba tare da ta sanar da ni ba.

"Kwatsam kawai sai tsohon saurayinta ya fara kawo mata ziyara a gidana musamman duk lokacin da na fita aiki.

"Bayan qanqanin lokaci Baraka ta sake daukar wani ciki kuma babu kunya sa ta kwashe kayan ta ta bar gida ne wai domin na dena kwanciya da ita a lokacin hakan yasa ta fara bawa yaron mu custard da madara, Inji Abdulrazak.

Abdulrazaka ya kara da cewa duk lokacin da ya tafi zuwa ganin ta domin ya bata kudin abinci ya kan tarar da saurayin a dakinta hakan ya sa ya tabbatar Barakat makaryaciya ce.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: