Monday, 15 October 2018

Majalisar dokokin jihar Kano tasamar da kwamiti bincike kan bidiyo da ke nuna ganduje da karbar "cin hanci"

Majalisar jihar Kano za ta fara binciken bidiyon Ganduje


Majalisar dokokin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta kaddamar da kwamiti na mutum bakwai domin yin bincike a kan wasu jerin bidiyo da ke ikirarin nuna gwamnan jihar da karbar "cin hanci" daga wajen wasu 'yan kwangila.

A makon da ya gabata ne jaridar Daily Nigerian da ke wallafa labaranta a intanet ta saki labarin da ke cewa wani gwamna a yankin arewa maso yammacin kasar wanda ke neman zarcewa a mulki karo na biyu, yana karbar makudan kudade a wajen wasu 'yan kwangila.

A ranar Lahadi ne kuma mawallafin jaridar Ja'afar Ja'afar ya saki bidiyo na farko daga cikin kusan 15 da ya ce yana da su, a shafin jaridar tasa.

Sai dai gwamnatin jihar Kano ta musanta wannan zargi.

Wani dan majalisar dokoki da ke wakiltar karamar hukumar Warawa Alhaji Labaran Abdul Madari ne ya gabatar da bukatar a yi bincike kan lamarin duba da muhimmancinsa, inda kuma dan majalisa mai wakiltar mazabar birni da kewaye Alhaji Baffa Dan Agundi ya goyi bayan hakan.

Honorabul Madari ya nuna cewa alhakin majalisar ne yin bincike a kan duk wani lamari da ya shafi jihar da zai iya yin barazana ga zaman lafiyarta.

Shugaban Majalisar Kabiru Alhassan Rurum ya bukaci kwamitin ya yi bincike sosai kan batun ya kuma gabatar da rahotonsa cikin wata guda.

Shugaban masu rinjaye Honorabul Baffa Babba Dan Agundi ne zai jagoranci kwamitin, da kuma sauran mambobi Zubairu Massu da Garba Ya'u Gwarmai da Abdulaziz Garba Gafasa da Abubakar Uba Galadima da kuma Barista Mujitaba Aminu wanda zai zama sakataren kwamitin.

Mafi yawan 'yan majalisar dai sun nuna goyon bayansu kan wannan bincike da za a yi.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: