Sunday, 7 October 2018

MALAM MENENE HUKUNCIN WANDA YAKE WASA DA AZZAKARINSA HAR MANIYYI YA FITO??? KO KUMA MATAR DA TAKE SANYA YATSA ACIKIN FARJINTA???


Yin haka bai halatta ba. Kuma yana daga cikin MANYAN LAIFUKA A MUSULUNCI.
Yana janyowa mai yin hakan FUSHI DA KUMA TSINUNWA DAGA UBANGIJI (SWT).
Manzon Allah (saw) yana cewa:

"MUTUM BAKWAI, ALLAH YATSINE MUSU. KUMA BA ZAI DUBE SU DA RAHAMA BA ARANAR ALQIYAMAH. KUMA ZAI CE MUSU: "ku shiga wuta tare da masu shigarta".

1. WANDA YAKE YIN LUWA'DI.
2. WANDA AKE YIN LUWA'DIN DASHI.
3. MAI YIN ZINA DA DABBOBI.
4., 5, 6, MAI YIN ZINA DA UWA, SANNAN KUMA YAYI DA 'YARTA.
7. MAI YIN ZINA DA HANNAYENSA (mai yin wasa da azzakarinsa
da kuma Mace Mai yin Hakan ga al'aurarta).

Sannan Kuma Shi irin wannan Aikin yana daga cikin irin Laifukan da Mutanen Annabi Lut (as) Suke yi.

* An Ruwaito cewar Duk masu yin haka idan basu tuba ba, ZASU TASHI ARANAR ALQIYAMA HANNAYANSU SUN DAUKI CIKI (juna biyu).

* Likitoci MaSu ilimin Sanin Lafiyar jikin Bil-Adama sun fadi wasu Illoli da dama wadanda yin hakan yake haifarwa:

1. MANTUWA MAI TSANANI. (mantuwar karatu, etc).
2. RAUNIN IDANU: masu yinhakan idan basu dena ba, sukan makance kafin wani lokaci mai nisa.
3. RAUNIN AL'AURA: Duk masu yin haka, idan suka yiaure, Sukan yi fama da rashin karfin Azzakari, saboda duk Maniyyin da aka fitar dashi da-gan-gan, Ba ya fita gaba-daya.
Wannan wanda ya saura, Sai ya daskare Maka acikin Mararka.
4. RASHIN HAIHUWA: Wannan daskararren Maniyyin, yana kashe kwayoyin halitta daga jikinNamiji ko mace..
5. CIWON HAUKA: da kuma Kaskanci.
Wannan dan kadan na Tsakuro daga cikin Irin illolin da wannan Al'amari yake haifarwa Ajikin Mata da Maza.
Da fatan Allah ya shiryi DukMasu yi su dena.

(WALLAHU A'ALAM).

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

1 comment: