Saturday, 6 October 2018

Yamutsin Kujerar Sanatan Kaduna ta Tsakiya: Shehu Sani ne dan takarar jam’iyyar APC – Uwar Jam’iyya



Duk da kai ruwa rana da aka yi ta yi a tsakanin shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole da reshen jam’iyyar a Jihar Kaduna kan tsayar da sanata Shehu Sani dan takara tilo da zai cira tutar APC a zaben Sanata na Shiyyar Kaduna ta tsakiya, har yanzu dai bata sake zani ba.

Duk da cewa akwai rahotanni da ya karade kafafen yana labarai tun daga ranar Alhamis din da ya gabata cewa wai jam’iyyar APC ta amince duk wanda ya sayi fom din takara ya fito yin zaben fidda gwani na kujerar sanata na shiyyar a Kaduna ranar Asabar, 6 ga wata, jam’iyyar ta ce bata san da haka ba.

Bayanan wannan takarda da mai taimakawa gwamna El-Rufai kan harkar siyasa, Uba Sani ya fitar sun nuna cewa ganawar shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya yi nasara inda shi gwamnan ya nemi a sauya wannan shawara na amincewa da dan takara daya tilo, a kyale duk sauran ‘yan takara su fafata a zaben fidda gwanin.

Wani jami’in gwamnatin jihar Kaduna da baya so a fadi sunan sa, ya bayyama mana cewa tabbas shi kan sa shugaban jam’iyyar APC Adam Oshiomhole ya aika wa El-Rufai sako na tes, ya na rokon sa da ya yi hakuri bisa abin da ya faru cewa yanzu za ayi zaben fidda gwani tsakanin ‘yan takarar da suka sayi fom.

Sai dai kuma, da muka nemi ji kai tsaye daga uwar jam’iyyar APC ta kasa, cikin gaggawa da kakkausar murya APC din ta karyata wannan sanarwa.
Yekini Nebena, kakakin jam’iyyar, ya karyata wannan labari cewa jam’iyyar APC na nan kan bakanta na dan takara daya ne tilo ta amince da yayi takarar Sanata na shiyyar Kaduna ta Tsakiya.

” Wannan sanarwa da ake ta yadawa ba daidai bane kuma bamu san daga inda ya fito ba. Mu dai a matsayin mu na uwar jam’iyya bamu san da wannan batu ba. Mutum daya ne muka amince wa zai cira mana tuta a zaben kujerar sanata ta Kaduna ta tsakiya, wannan mutum kuma shine sanata Shehu Sani.” Inji Kakakin APC, Nabena.

A safiyar Asabar, mai taimakawa Sanata Shehu Sani kan harkar yada labarai, Abdussamad Amadi, ya sanar cewa ba su tare da masu shirya zaben fidda gwani da ake shirin yi a jihar ranar Asabar din.

” Muna sanarwa mutanen shiyyar Kaduna ta tsakiya cewa mu masu biyyane ga jam’iyya, babu ruwan Sanata Shehu Sani da wannan zabe kuma magoya bayan mu su nisanta kansu daga wannan zaben.” Inji Amadi.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: