Saraki na fuskantar matsin lamba kan cewa ya janyewa Atiku
Rahotanni dake bullowa gare mu sun yi ikirarin cewa shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki na fuskantar matsin lamba kan cewa ya hakura da kudirinsa na takarar kujerar shugaban kasa sannan ya marawa Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa baya don ganin ya samu tikitin takarar shugabancin kasa na PDP.
A cewar shafin, Sahara Reporters, wata majiya na daya daga cikin makusantar ýan takarar ya bayyana cewa Atiku na ta tattaunawa da sauran yan takara irin su Saraki.
Majiyar tace: “Atiku na ta tattaunawa da sauran yan takara irin su Saraki tare da burin ko zasu janye nasu kudirin,don filin ya zama na Atiku da Tambuwal a babban taron jam’iyyar.
“Bana tunanin zai amince amma abun da na sani shine yana fuskantar matsin lamba,”inji majiya na biyu wanda ya nemi a boye sunan sa.
“An matsa masa; ana ta tattaunawa, sannan ana ta magana kan ya hakura ya janyewa Atiku.
Tsohon Mataimakin shugaban kasar na kokari gina hadin gwiwa; idan Saraki ya janye masa, hakan na nufin zai samu dama saboda wakilan Saraki zasu koma bayansa.
“Ban san abinda Saraki zai yanke ba, amma zan iya tabbatar a cewa eh yana fuskantar matsin lamba don ya janye wa Atiku - A cewar Majiyar
0 comments: