Friday, 5 October 2018

Rundunar Jami’an Kwastam Ta Kasa Sun Kama Kayan Sojoji


Babban jami’in Controller Zone A Ikeja Lagos Alhaji Aliyu Muhammad ya gabatar da bayanin cewa jami’ansa sun kama kayan sojoji masu yawan gaske wanda aka kama a cikin mota kirar bus mai dauke da namba kamar haka JJT 905 XB motar mallaki wani kamfani mai suna Chimezie Motors Nigeria Limited

Controller Aliyu Muhammad yace wasu jama’a ne a jihar Lagos suka taimaka da bayanan sirri wanda ya kai ga bin diddigin motar har aka samu nasaran kama kayan sojojin, ya kara da cewa wannan babban barazanace ga tsaron kasa, kuma suna cigaba da gudanar da bincike

Idan irin wannan abu ya faru muna kira ga mahukuntan Nigeria su fadada bincike duk wanda yake da hannu a samar da kayan sojoji haramtattu su fuskanci hukuncin da ya dace, a tsakanin wata daya wannan shine kusan karo na biyar da jami’an Kwastom suke kama haramtattun kayan sojoji, kuma har yanzu bamuji labarin wanda aka hukunta ba

Gashi ana fama da matsala da barazana na tsaro a Jos, rikici yana tashi a Jos ana zargin akwai jami’an tsaron bogi wadanda suke saka kayan sojoji da na ‘yan sanda su hau motoci kirar hilux da bindigogi suna bi gidajen musulmai suna hallakasu, dole a tsaurara bincike ayi hukuncin da ya dace
Allah muna rokonKa ka cigaba da tona musu asiri

Allah Ka bamu zaman lafiya a Nigeria


SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: