Sunday, 14 October 2018

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya fitar da wata doka da ta haramtawa wasu 'yan kasar su 50 fita kasashen waje.


Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari,
ya fitar da wata doka da ta haramtawa wasu 'yan kasar su 50 fita kasashen waje.

Wadannan mutane ana tuhumar su ne da yin ruf-da-ciki da kudin kasa, abin da ya sa aka umarci jami'an tsaro da su sa ido a kan su don kar su samu damar sulalewa su bar kasar.

Mai magana da yawun shugaban kasar kan harkokin watsa labarai, Malam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa, shugaban kasar ya dauki matakin ne bisa la'akari da cewa akwai wadanda gwamnati da kuma sassa daban-daban na bincike na
hukumomin Najeriya ke gudanar da bincike a kan wasu makudan kudade a gida da waje, abin fargabar inji Garba Shehu, shi ne kada su je su salwantar da wadannan kudade kamar yadda ya faru da wasu a baya.

Garba Shehu, ya ce to dakatar da su daga zuwa wajen inda suka ajiye ko boye wannan dukiya a waje saboda kada su salwantar da ita ta yadda ba bu wanda zai amfana, shi ya sa aka fitar da dokar.

Mai ba wa shugaban Najeriyar shawara, ya ce zirga-zirgar da aka hana irin wadannan mutane, na da tasiri a shari'ance.
Garba Shehu ya ce duk wanda ya san bai dauki kayan jama'a ya mallakawa kansa ba, to ba shi da wata fargaba dangane da wannan sabuwar doka.

A wani labarin kuma, tuni dai babbar jam'iyya adawa a Najeriya PDP, ta yi watsi da da matakin da shugaban kasar ya dauka na sanya hannu kan wata doka da ta haramta wa wasu 'yan kasar su 50 fita waje, saboda zargin cin hanci da rashawa.
Jam'iyyar ta yi zargin cewa an kafa dokar ne don takura wa wasu 'yan PDP da za su iya kawo cikas ga takarar shugaba Buhari a zabe mai zuwa.

Tuni dai kungiyoyin da ke fafutukar yaki da rashawa suka ce wannan mataki da shugaban Najeriyar ya dauka na kafa dokar haramta wa wasu 'yan kasar fita kasashen waje ta yi dai-dai.

Malam Abdulkarim Dayyabu, shi ne shugaban rundunar Adalci ta Najeriya, ya kuma shaida wa BBC cewa, wannan mataki da aka dauka abune da yakamata, har ma na so a makara wajen daukarsa.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: