Najeriya ta doke Libya da ci 4 - 0 a karawarsu.
Najeriya ta doke Libya 4 - 0 a karawarsu da Libya a wasansu na rukunin na 5 na gasar cin kofin Afirka (AFCON) wanda aka yi yau Asabar 18 ga Oktoba a filin wasa na Uyo da ke jihar Akwa Ibom.
Odion Ighalo ya zura kwallo uku, inda shi kuma Samuel Kalu ya jefa daya.
Kungiyar Super Eagles ta Najeriya ta fara wasan da kafar dama bayan da alkalin wasa ya basu bugun fenariti a minti uku na fara wasan bayan da aka kayar da Odion Ighalo.
Ba tare da bata lokaci ba, Ighalon ya zura kwallo ta farko a ragar Libya.
Haka aka tafi hutun rabin lokaci ana Najeriya 1, Libya 0.
Da aka dawo hutun rabin lokaci, sai Ahmed Musa ya fara matsa wa golan Libyan, amma bai sami zura kwallo ba.
Amma matsin yayi amfani, domin ba a dade ba sai Odion Ighalo ya jefa kwallo ta biyu bayan da Alex Iwobi ya aika masa da wani kuros wanda ya mayar da wasan Najeriya 2 Libya 0.
Daga nan kuma sai Igahlo ya zura kwallo ta uku bayan da Ahmed Musa ya aika masa da wani kuros wanda ya dawo masa kuma kai tsaye ta shiga ragar Libya.
Shi kuma Samuel Kalu ya zura kwallo ta hudu bayan da ya murda wani shot da golan Libya ya kasa kamawa bayan da ya karbi fas daga Henry Onyekuru.
Nasarar Super Eagles a wannan wasan na nufin sun lashe wasanni biyu a jere kenan, kuma sun hada maki shida.
Wasan Super Eagles na gaba zai faru ne a Tunisia inda kungiyar za ta kara da Libya a karo na biyu ranar Talata 16 ga watan Oktoba.
0 comments: