Sunday, 13 January 2019

Ayi hattara 2019: Ba zamu bari APC ta murde zaben shugaban kasa ba - Atiku

Ayi hattara 2019: Ba zamu bari APC ta murde zaben shugaban kasa ba - Atiku

Alhaji Atiku Abubakar, ya ce PDP zata dauki duk wasu matakai da ya dace don dakile jam'iyya mai mulki ta APC daga tafka magudi a zabe mai zuwa

Ya ce PDP zata tabbata ta kawo karshen rikici da ta'ddancin da ake yi a jihar Filato da zaran an zabeta

APC, a cewar Atiku, ta haddasa asarar guraben ayyukan mutane da dama sakamakon wani mummunan tsarin tattalin arziki da ta dauka
Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP

Alhaji Atiku Abubakar, ya ce jam'iyyarsa zata dauki duk wasu matakai da ya dace don dakile jam'iyya mai mulki ta APC daga tafka magudi da zaben shugaban kasa na watan Fabreru, 2019 da ke gabatowa.

Da yake jawabi ga dandazon jama'ar da suka taru a gangamin yakin zabensa a Jos, Atiku ya ce tuni APC ta yanke shawarar tafka magudi kuma wannan ne ma dalilin da ya sanya basa yin yakin zabe a fadin kasar kamar yadda PDP take yi.

Ya ce PDP zata tabbata ta kawo karshen rikici da ta'ddancin da ake yi a jihar Filato da zaran an zabeta, kana ya bukaci daukacin masu kada kuri'arsu a jihar dasu zabi dan takarar jam'iyyar, Sanata Jeremiah T. Useni a matsayin gwamnan jihar.

APC a cewar Atiku, ta haddasa asarar guraben ayyukan mutane da dama sakamakon wani mummunan tsarin tattalin arziki da ta dauka, kuma PDP zata wanke duk wani datti da APC ta kawo tare da samar da ayyukanyi, ma damar aka zabeta.

A jawabinsa, shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya ce tuni APC ta haddasa wani rikici da kuma karya dokoki inda har ta samu nasarar raba kawunan majalisar tarayya, yana mai cewa ci gaba da gallazawa da tsare Sanata Dino Melaye na daga cikin yunkurin gwamnatin na rufe bakin 'yan majalisun tarayyar.

Shima da yake jawabi, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus, ya ce ba zasu lamunci ta'addanci a zabe mai zuwa ba.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: