Haramta shan barasa a jihar Kano ba ya cin karo da kundin tsarin mulkin Najeriya
A kwana-kwanan nan mun kawo muku rahoton yadda hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta tarwatsa wasu kwalabai na barasa makire cikin motoci 30 ma su dakon kaya. Wannan lamari ya janyo cecekuce tare da ci gaba na barin baya da kura,
Shugaban hukumar Hisbah na jihar, Dakta Abba Sufi, shine ya labarta wannan lamari yayin amsa tambayoyin manema labarai da cewa, gwamnatin jihar Kano ta dauki wannan salo na harama fatauci da ta'ammali da barasa tun a shekarar 2004 da ta gabata,
Dakta Sufi yayi furucin hakan ne a yayin mayar da martani dangane da yadda lamarin haramta barasa a jihar Kano a halin yanzu yake ci gaba da barin baya da kura gami da fuskantar cecekuce musamman a mahanga ta kundin tsarin mulkin Najeriya.
Wani fitaccen lauya mazaunin jihar Legas mai kare hakkin bil Adama, Mista Ebu-Olu Adegboruwa, ya ce tsarin dokokin gwamnatin jihar Kano na haramta fatauci da ta'ammali da barasa na cin karo gami da sabawa kundin tsarin mulki na kasar nan,
Mista Adegboruwa ya hikaito yadda sashe na goma cikin kundin tsarin mulkin
Najeriya ya haramtawa kowace jiha riko da kowane nau'i na addini da a halin yanzu jihar Kano ke ribatar shari'ar addinin musulunci wajen haramtawa al'umma 'yancin su na rayuwa.
Cikin zayyana damuwar sa Mista Adegboruwa ya ce, tsantsar siyasa ta neman suna da samun shiga wurin al'umma ya sanya jihar Kano ta zartar da wannan danyen hukunci yayin da babban zabe ya gabato.
A yayin ci gaba da raddi gami da mayar da martani, shugaban hukumar Hisban ya ce, gwamnatin jihar Kano na dama a bisa tanadi na kundin tsarin mulkin Najeriya ta shimfida dokoki daidai da kare martabar dabi'un al'ummar ta.
0 comments: