Buhari zai kaddamar da hakar man fetir a jahar Gombe
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da fara hakan man fetir a jahar Gombe a ranar Asabar, 2 ga watan Janairu, wanda hakan zai shigar da jahar Gombe cikin jerin kasashen Najeriya dake da arzikin man fetir,
Shugaba Buhari zai kaddamar da hakan man ne a yankin tafkin Kolmani, wani sashi dake tsakanin jahar Gombe da jahar .Bauchi, kamar yadda hukumar man fetir na Najeriya, NNPC ta sanar,
Babban manajan watsa labaru na hukumar NNPC. Ndu Ughamadu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a, 1 ga watan Janairu, inda yace shugaba Buhari zai kaddamar da aikin ne tare da hadin gwiwar shugaban NNPC, Maikanti Baru,
Yankin da za’a kaddamar da hakan man fetir din, tafkin Kolmani II, yana kusa da kauyen Barambu dake cikin karamar hukumar Alkaleri na jahar Bauchi, haka zalika Mista Ndu yace an soma hakan man fetir dinne sakamakon wasu sabbin dabaru da shugaban NNPC. Maikanti ya zo dasu.
Makasudin samar da wadannan dabaru shine domin kara adadin danyen mai da iskar gas da Najeriya take fitarwa, samar da isashshen man fetir a Najeriya.
samar da karin kudin shiga ga gwamnati da kuma samun karin wuraren hako mai a yankin Arewa,
A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai isa jahar Gombe a ranar Asabar, 1, ga watan Feburairu domin cigaba da yakin neman zabensa na takarar shugaban kasa a karo na biyu.
Friday, 1 February 2019
Author: Adamu umar
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: