Jam'iyyar PDP ta bukaci INEC ta haramtawa Buhari shiga zaben 16 ga watan Fabreru
Jam'iyyar adawa ta PDP ta bukaci INEC da ta cire sunan Buhari da ga 'yan takarar kujerar shugaban kasa a zaben ranar 16 ga watan Fabreru mai zuwa.
PDP ta yi zargin cewa Buhari da APC sun shigo da bakin haure daga kasashen waje domin taimaka masa wajen samun nasarar zabe mai zuwa
Gwamnoni biyu daga jamhuriyyar Niger, na daga cikin wadanda suka halarci kaddamar da yakin zaben Buharin a jihar Kano
Jam'iyyar adawa ta PDP ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da ta cire sunan shugaban kasa Muhammadu Buhari da ga 'yan takarar kujerar shugaban kasa a zaben ranar 16 ga watan Fabreru mai zuwa,
Uche Secundus, shugaban jam'iyyar PDP na kasa, ya yi wannan kiran a lokacin kaddamar da yakin zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Alhaji Atiku Abubakar, a jihar Enugu da ya gudana a ranar Juma'a,
Ya yi zargin cewa shugaban kasa Buhari ya kawo bakin haure daga kasashen waje domin murde zaben mai zuwa da nufin bashi nasara, a lokacin da ya kaddamar da yakin zabensa na jihar Kano.
gwamnoni biyu daga jamhuriyyar Niger, da suka hada da Issa Moussa na jihar Zinder da kuma Zakiri Umar na jihar Maradi, suna daga cikin wadanda suka halarci kaddamar da yakin zaben Buharin a jihar Kano
Secondus ya bukaci al'ummar jihasr Enugu da su fito kwansu da kwarkwatasu domin zabar Atiku Abubakar, wanda ba zai runtsa akan yiwa kasa aiki ba, yana mai cewa "PDP jihar Enugu ce haka zalika jihar Enugu itama PDP ce."
"Yanzu a madadin jam'iyyarmu mai albarka, bari na gargadi INEC, ta sani cewa munga yadda yakin zaben Buhari ya kasance a jihar Kano, wanda ba a taba samun lalataccen taro a tarihin siyasa irinsa ba, inda har jami'an gwamnati ke dauko hayar wasu mutane daga wata kasa domin su cika wajen taron da kuma yunkurin shiga harkokin zaben kasar," a cewar Secondus,
"Sun shigo da kudi da kuma wasu alatu domin yaudarar 'yan Nigeria. Ku duba, kusan gaba daya jaridun kasar sun wallafa wannan labarin.
"Yanzu sai mu bukaci INEC ta cire son kai, ta cire sunan Buhari daga 'yan takarar shugaban kasa, saboda shigo da bakin haure kasar da nufin kawo tangarda da murdiya a zabe mai zuwa."
A nashi jawabin, Atiku ya bukaci al'ummar Igbo da su zabe shi, domin samun mataimakin shugaban kasa da ya fito daga shiyyarsu.
Saturday, 2 February 2019
Author: Adamu umar
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: