Jonathan Nda-Isiah na Jaridar Leadership ya kawo abubuwan da ke gaban Shugaba Buhari da zarar ya dawo gida.
1. Sauya mukaman Gwamnati
Da zarar Shugaba Buhari ya dawo ana sa ran ya sauya wasu Ministoci ya kuma nada wasu kamar yadda mu ka kawo a baya.
2. Nade-naden mukaman Gwamnati
Akwai mukamai na Ma'aikatun Gwamnati da har yau ba a nada ba duk da cewa an ci fiye da shekaru 2 a mulkin.
3. Sabon Sakataren Gwamnati
A kwamitin da Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta bayan an dakatar da Sakataren Gwamnati Babachir Lawal an nemi a tunbuke sa a kuma nada wani tare da hukunta sa.
4. Raba kasa
A halin yanzu wasu da dama na kokarin kawowa hadin kan kasar barazana. Mukaddashin Shugaban kasa yayi taron zama da Jama'a da dama daga fadin kasar a dalilin haka.
5. Tattalin arziki da Boko Haram
Shugaban kasa Buhari yayi alkawarin habaka tattalin arzikin kasar da kuma yaki da Boko Haram. Har yanzu dai tattalin arzikin kasar na tan-gal-tan-gal yayin da Boko Haram ke kokarin canza fasali.
Friday, 4 August 2017
Author: Arewarmu Concepts
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: