Friday, 4 August 2017

Sana'o'i 3 da su ka fi kowane kawo kudi a Duniya

Tun ba yau ba dai Likitoci sun yi kaurin-suna musamman kuma wajen karbar albashi mai tsoka a Duniya. Haka kuma Ma'aikatan mai ba a bar su a baya ba.

1. Likita

Likita musamman na Mahaukata da kuma mai fyede maras lafiya na cikin wanda ya fi kowa albashi a Duniya.

2. Injiniyan man fetur

A wasu wuraren a Duniya masu Dirgiri a wannan fanni na samun alal akalla Dala 130,000 a kowace shekara. Akwai kudi a harkar man fetur.

3. Na'ura mai kwakwalwa

Wadanda su ka karancin wannan ilmi su na cin karen su babbaka a Duniya don kuwa da su ake damawa yanzu.

Masu aikin tukin jirgin sama da kuma ilmin sarrafa magunguna ba a bar su a baya ba a magana da ake yi.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: