Tuesday, 8 August 2017

Babu dangantaka tsakanina da Rahama Sadau —Nafisa Abdullahi

Fitacciyar jarumar Kannywood Nafisa Abdullahi ta ce duk da yake sana'arsu daya da Rahama Sadau, babu wata alaka ta 'yan uwantaka ko kawance a tsakaninsu.
Nafisa, wacce ta bayyana haka a shafinta na Instagram, ta ce babu wata abokantaka tsakanin matan da ke yin fina-finan na Hausa.

A cewarta, "Ina mamakin yadda masu amfani da shafin Instagram ke daukar mu ['yan fim] wallahi. Ya kamata ku sani cewa da ni da Rahama sana'armu guda, amma babu abokantaka ko 'yan uwantaka tsakanimu. Kai, babu wata dangantaka tsakaninmu mata 'yan fim. Don haka, duk wanda yake tunanin muna jituwa yaudarar kansa kawai yake yi."

Jarumar ta yi ikirarin kowa ta kansa yake yi tsakanin 'yan kannywood, tana mai cewa lokacin da wani ya wallafa hotonta sanye da gajeren wando—batun da ya janyo mata zage-zage—babu wata 'yar Kannywood da ta fito ta kare ta duk da yake sun san cewa an yi ne domin a bata mata suna.

Ta kara da cewa ta yi amanna Rahama za ta iya jure wa halin da ta fada a ciki, sannan ta yi kira ga mutanen da ke son ta bi sahun masu kiraye-kirayen a janye korar da aka yi wa Rahama su daina bata lokacinsu.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: