Tuesday, 8 August 2017

Zan Ci Gaba Da Tallafa Wa Marayu - inji Nafisa Abdullahi

A ranar Juma'ar makon da ya gabata Ranar 23 ga Watan Augusta 2015 ne shahararriyar jarumar finafinan Hausan nan Nafisa Abdullahi, wadda aka fi sani da ‘Sai Wata Rana’ ta kai ziyara gidan marayu da ke unguwar Barnawa a jihar Kaduna da kuma daya daga cikin gidajen marayu na Kano, inda bayan ta gana da su, ta yi musu goma ta arziki, ta ba su kayan abinci da kayan sanyawa, sannan kuma ta yi musu fatan alkari tare da karfafa musu gwuiwa.
Hoton ziyarar jarumar da ya soma yawo a kafafen sadarwar zamani da suka haxa da facebook, Instagram, twitter da sauransu, an nuno jarumar dauke da xaya daga cikin marayun, da kuma wanda ta yi tare da dandazon marayun da kuma kayan masarufin da ta saya ta kai musu.

A yayin da Arewarmu.com ta ji ta bakin jarumar ta waya kana bin da ya ja hankalinta ga yin hakan, Nafisa ta ce “ai wannan abu ne wand aba sai wani abu yaba ka sha’awa ko jan hankalinka ga hakan ba. Kuma na jima ina da sha’awar son zuwa gidan marayu da asibitoci da makamantan haka”.
Nafisa ta ce wannan shine karo na farko da ta soma yin hakan, amma kuma bas hi zai zamo na qarshe ba, domin za ta ci gaba da gudanar irin waxannan alkairi.

Bayan labarin ya soma yaxuwa a kafafen sadarwar, Nafisa ta yi ta shan ruwan addu’o’in fatan alkairi bisa abin alkairin da ta yi wa marayun, musamma ma ganin shine kusan na farko da wata jaruma ta yi hakan, sannan kuma an ja hankalin takwarorinta musamman maza da su dinga kwatanta alkairi makamncin haka.
“Tabbas wanda abin alkairi da jarumar ta yi abin a yaba ne, domin ba kowane yake da irin wannan tunani da tausayin ba, don haka ina jan hankali sauran abokan sana’arta da ma sauran jama’ar da ke da damar yin hakan da su tashi tsaye wajen ganin suna taimakawa marayu, wadanda sun kasance ba su da iyaye”, kamar yadda wani daga cikin waxanda suka yaba da abin alkairin da jaruma Nafisa ta yi wa marayun.

Nafisa Abdullahi dai tauraruwarta ta soma haskakawa ne a fim, tun daga lokacin da ta yi fim din ‘Sai Wata Rana’ na kamfanin FKD shekaru kusan shida da suka gabata, duk da cewa ba shine fim na farko da ta soma fitowa a ciki ba.

Wannan Labari ba Sabo bane Domin ya farune tun a shekarar 2015, mun kawo Muku shine don sanar daku irin gudummuwar da Jaruma Nafisa Abdullahi Ta bayar.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: