Friday, 4 August 2017

Ka ji abin da Gwannan Kuros-Riba yayi wa Malaman musulunci

Mun ji labarin cewa Gwamnan Jihar Kuros-Riba Farfesa Ben Ayade ya sakawa Limaman Jihar sa da irin alherin da su kayi masa.
Gwamna Ben Ayade ya cika alkawarin sa da yayi wa Malaman Addinin Musulunci a Jihar inda ya ba su kudi Naira Miliyan 10 a dalilin addu'o'in da aka rika yi masa lokacin yana yakin neman zabe da kuma neman nasara a Kotu bara.
Shugaban Malaman Jihar Kabir Saad Ibrahim ya bayyanawa Jaridar Daily Trust wannan yace Gwannan bai yi kasa a gwiwa ba kuma za su cigaba da yi wa Gwamna Ben Ayade da Shugaban kasa Muhammadu Buhari addu'a tare da kokarin hada kan Jama'a.

Kwanaki Gwamnan Jihar Kuros Riba Ben Ayade yace shi da mutanen Jihar sa sun dage ba dare ba rana wajen yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a ya samu lafiya.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: