Shahararriyyar jarumar nan ta wasan fina-finan Hausa na Kannywood watau Hafsat Idris ta bayyana sana'ar fim a matsayin muhimmiyar sana'ar da ta ke rufa mata asiri tare da iyayen ta.
Jarumar ta yi wannan ikirarin ne a cikin wata fira da tayi da wakilin majiyar mu lokacin da take ansa tambayoyi daga gare shi.
Arewarmu.com ta samu labarin cewa jarumar dai ta fara fim ne a watan Disambar shekarar bara ta 2016 sannan kuma dalilin yin fim din nan nata na Barauniya ya sa masu hada fina-finai na yin ruguguwar sanya ta a fina-finansu saboda yadda ta kware a lokaci guda.
Haka ma dai jarumar ta bayyana cewa kowanne wata takan yin fina-finai akalla 3 zuwa 4 saboda amincewar da furodusoshi suka yi mata wajen taka rawa a manyan fina-finai.
Thursday, 3 August 2017
Author: Arewarmu Concepts
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: