Thursday, 3 August 2017

Wata Sabuwa: Ana caca a kan Dawowar Shugaba Buhari a Nigeria

Wasu 'yan Najeriya sun soma yin caca a kan ranar da shugaban kasar Muhammadu Buhari, wanda ya shafe kusan wata uku yana jinya a birnin London, zai koma kasar.

Wani shafin intanet da ke yin caca, NaijaBet.com, na tambayar mutanen da ke da sha'awar cacar su canki ranar da shugaban kasar, wanda ya fice daga Najeriya ranar bakwai ga watan Mayu, zai koma gida.

A watan Yunin shekarar 2016 ne shugaban, mai shekara 74 a duniya, ya soma tafiya London domin yin jinyar abin da, a wancan lokacin, jami'an gwamnati suka bayyana da ciwon kunne.
A farkon wannan shekarar ma Shugaba Buhari ya koma London inda aka duba lafiyarsa.

A lokacin da ya koma kasar a watan Maris, ya ce an yi masa karin jini, ko da yake bai fadi larurar da yake fama da ita ba.

Sai dai shugaban na Najeriya ya ce bai taba yin jinya irinta ba a rayuwarsa.

A watan jiya ne mukaddashin shugaban kasar Yemi Osinabjo ya ziyarci Shugaba Buhari a London, kuma ya ce shugaban yana samun sauki.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: