Tsohon shugaban kasa ya bayyana abubuwa uku muhimmai da su ke kawo wa cigaban kasar nan cikas kuma ya ce ba tsare-tsare bane ba bu sai dai hanyar gudanarwar ke da matsala
A ranar larabar da ta gabata ne tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yi tsokaci a kan yadda gwamnatin tsohon shugaban kasa, Marigayi Umaru Yar'Adua ta yi watsi da tsare-tsaren gwamnatin sa.
Obasanjo ya yi wannan tsokaci a yayin da ya je taron kaddamar da wani littafi wanda har da shi a cikin marubata littafin a tsibirin Victooria da ke jihar Legas.
Tsohon shugaban kasar ya ce ainihin matsalar da ke kawo wa Najeriya da ma kasashen Afirka tangarda ba karancin tsare-tsare ba ne sai dai hanyoyin gudanar da tsare-tsaren sanadiyar rashin shugabanci nagari.
Ya ce manyan matsalolin da ke kawo wa kasar nan cikas ba su wuce guda uku ba wanda su ne shugabanci, dorar da aiyukan tsohuwar gwamnati da harkokin kudi.
Obasanjo wanda marigayi Yar'Adua ne ya gaji kujerar sa ta shugabancin kasar nan kuma dukkannin su 'yan jam'iyyar PDP ne ya bayyana cewa gwamnatin Yar'Adua ta yi watsi da tsare-tsaren da gwamnatin sa ta kawo wanda idan da an cigaba da su to tabbas za a ga canji.
Ya cigaba da cewa akwai tsarin NEEDS (National Economic Empowerment and Development Strategy) da gwamnatin shi ta kawo wanda zai cire Najeriya daga cikin kangin da ta ke ciki kuma gwamnatin ta samu yardar shugabanni na kowane bangare a kasar a kan wannan tsari.
An fara gudanar da wannan tsari a karon farko amma gwamnatin da ta gaje shi sai ta yi watsi da wannan tsari ta kawo na ta tsare-tsaren wanda ba za su kai mu ko ina ba kamar tsarin samar da wutar lantarki cikin shekaru 4 wanda a karshe ma sai siyar da kamfanin wutar lantarkin a ka yi ga 'yan kasuwa wanda su kansu ba su san ya za su yi da shi ba.
Ya ce daya daga cikin matsalolin kasar nan shi ne rashin dorawa daga aikin da tsohuwar gwamnati kuma ya ce in dai haka za a cigaba babu inda kasar nan za taje don ga harkar wutar lantarki, yadda ya barta shekaru goma baya haka ta ke har yanzu ba bu wani canji.
A karshe Obasanjo ya ce muddin a na son kawo karshen rashin cigaban da ke yi wa Najeriya katutu sai an gyara tsarin shugabancin kasar nan da kuma cigaba da dorawa a kan tsarin aikin tsohuwar gwamnati.
Thursday, 3 August 2017
Author: Arewarmu Concepts
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: