Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ba zai yi murabus ba saboda bai karya kowani doka saboda ya kai kwanaki 90 da zama birnin Landan.
Shugabankasa ya yi jawabin ne a ranar Litinin ta hanyar mataimakin sa na Harkokin Watsa Labaru da Gargajiya Malam Garba Shehu.
Shehu, a wata ganawar da ya yi da yan jarida, ya ce wadanda ke kiran shugaban kasa ya yi murabus, ba su san dokar kasa ba.
Ya fada ra’ayin sa akan zanga-zangan da kungiyoyin farar hula suke yi akan zaman shugabankasa a birinin Landan.
Ya ce zanga-zangan bai da amfani saboda Buhari ya mika mulki ga mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo kafin tafiyar sa ya kuma rubuta wa Majalisar Dokoki na kasa.
Mutane suna da daman fitowa suyi zanga-zanga saboda hakkin ne da kudin tsarin mulki ya basu, menene amfani dimokradiyya idan yan kasa baza su iya zanga-zanga ba? Muna girmama hakkinsu na yin zanga-zanga amma suyi shi a cikin lumana.
“ A batu na biyu shi ne, kira da shugabankasa yayi murabus, ko ya bayyana abun dake damu sa, wanna ya fita daka tsarin dokar kasannan. Duk wanda yasan dokar kasannan sosai zai lura da ce wa shugaban kasa ya cika kasha 100 cikin 100 na bukatin kundin tsarin kasa."
Ya mika wa mataimakinsa mulki kaman yadda doka ta tabbatar, mataimakin shugaban yana gudanar da harkokin kasar nan da kyau,kaman yarda shugaban kasa zai yi.
“Saboda haka shugaban kasa bai karya kowani doka ba. Duk abin da yayi, yayi daidai da tsarin mulkin Najeriya. Mutane suna neman abun fada ne kawai."
Shugaba Buhari ya ta fi Birtaniya ne a ranar 7 ga watan Mayu don ganin likitocinsa.
Tuesday, 8 August 2017
Author: Arewarmu Concepts
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: