Wasu kungiyoyin al'umma sun yi zanga-zanga suna kira ga shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ko dai ya koma aiki ko kuma ya sauka.
A ranar Litinin ne wasu kungiyoyin al'umma suka yi zanga-zanga suna kira ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ko dai ya koma aiki ko kuma ya sauka.
Masu zanga-zangar sun ce sun shirya ta ne ganin cewa shugaba Buhari ya shafe kwanaki 92 yana jinya a birnin London, kuma har yanzu babu wani bayani kan yanayin rashin lafiyarsa ko kuma lokacin da zai koma bakin aiki.
Wani mawaki mai suna Charly Boy ne ya shirya zanga-zangar wacce ba ta samu halartar mutane da dama ba.
Mutanen sun yi ta daga kyallaye da ke dauke da rubuce-rubuce da dama na neman shugaban ya sauka daga mulki.
Gomman masu zanga-zangar sun faro ne daga dandalin Unity Fountain da ke birnin tarayya Abuja, inda suka dire a kwanar shiga fadar shugaban kasa, bayan da jami'an tsaro suka dakatar da su.
Daga cikin kungiyoyin da suka halarci zanga-zangar har da kungiyar 'yan uwa Musulmai ta Shi'a da ke kira da a saki shugabanta Malam Ibrahim El-Zakzaky
MAsu zanga-zangar dai sun ce za su ci gaba da yin zaman dirshan a wajen har sai sun ga abin da ya turewa buzu nadi.
Monday, 7 August 2017
Author: Arewarmu Concepts
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: