Sunday, 6 August 2017

Ana Wata Ga Wata: Wani jigon jam’iyyar mai mulki ta APC ya sauya sheka zuwa PDP

Alhaji El-Amin Ibrahim, wani jigon dan siyasa a jama'iyyar mai mulki ta APC a jihar Kano, ya canza sheka zuwa jam'iyyar hamayya ta PDP.

Ibrahim ya gaya wa manema labarai a Kano a ranar Asabar, 5 ga watan Agusta cewa, ya yanke wannan shawarar ne domin taimakawa mutanensa da kuma tabbatar da cewa alkawuran da aka yi masu an cika su.

Dukanin sauya sheka da na yi a baya sun kasance daga jam'iyyu da ke karagar mulki zuwa jam’iyyun adawa kuma har sau uku Ina taimaka wa jam'iyyar lashe zabe.

“Ni ban shiga harkokin siyasa don amfanin kai na ko kuma domin in tara kudi ba ne. Na shiga ne domin na taimaka wa mutane na”. A cewar Alhaji El-Amin Ibrahim.

Ibrahim, wanda aka sanshi a matsayin Ibrahim-little, ya ce ya yanke shawara canza sheka zuwa jam’iyyar PDP saboda jam’iyyar mai mulki ta APC ta gagara cika alkawuran ta ga al’umma.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Ibrahim-little ya kasance tsohon shugaban tsohuwar jam’iyyar ta APP a jihar Kano da kuma tsohon dan takara gwamna a karkashin jam'iyyar a shekarar ta 2003.

Idan dai baku manta ba a ranar Asabar nan ne NAIJ.com ta ruwaito cewa tsohon gwamnan jihar Kano, sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kauracewa taron jam’iyyar mai mulki ta APC shiyar Kano.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: