Sunday, 6 August 2017

Zamu kawo Shekau nan da kwani 40 kamar yadda mukayi alkawari – Rundunar soji

Rundunar sojin Najeriya ta sha alwashin kaddamar da umurnin da Tukur Buratai ya ba ta na kamo shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, a raye ko a mace cikin kwanaki 40

A cewar Channels TV, Birgediya Janar Sani Usman wanda ya kasance kakakin rundunar sojin ne ya tabbatar da hakan a Buniyadi, jihar Yobe.

Hakan ta kasance ne a lokacin wani ganawar sirri da Buratai yayi da rundunar musamman rundunar sashi na 27.
Sojojin sun yaba ma Buratai kan aikinsa da kuma kulawarsa sannan kuma sun yi alkawarin cewa zasu kama Shekau cikin kwanaki 40.

A halin yanzu, Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti ya soki shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yawan hare-hare da ‘yan ta’addan Boko Haram ke kaiwa a kasar.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: