Friday, 27 July 2018

Allah mai iko: Za a gamu da husufin wata yau a Najeriya

- Yau rana za ta kama wata na fiye na awa guda a wasu bangarorin Duniya.

Mun samu labari cewa manyan Masana harkar taurari da yanayi sun bayyana cewa za a gamu da husufin wata yau. Farfesa Augustine Ubachukwu ya bayyanawa ‘Yan Jarida wannan a Garin Abuja.
Rana za ta kama wata a daren nan a wasu sashen Duniya Augustine Ubachukwu wanda Malami ne a Jami’ar Najeriya ta Nsulla ya bayyana cewa za a ga rana ta kama wata a cikin daren nan. Masanin yace wannan abu zai faru ne tsakanin karfe 9:30 zuwa kusan 11:22 na daren yau dinnan.


A bayanin da yayi wa manema labarai, babban Farfesan ya bayyana cewa husufin watan zai dauki lokaci kimanin sa’a guda a Najeriya. Wannan abu dai ba a Najeriya kurum zai faru ba domin zai shafi har Nahiyar Amurka ta Kudu.


Za a fi ganin bayyanar husufin ne a Nahiyar Turai da kuma Kasashen Ustaraliya da kuma Yankin Asiya da Kasar New Zealand da kuma nan Afrika. An dai fi shekara 100 ba a taba samun husufin da zai dauki kusan awa guda ba a Duniya.

A kan samu kusufin ne idan har rana ta kama wata a cikin daren da wata ya cika. Kasar New Zealand ce za ta fara ganin wannan abin mamaki jim kadan bayan faduwar rana inji Masanan.

To Allah yarufa Asiri #Ameen

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: