Saturday, 28 July 2018

Jaruma Zainab Indomie: Tana shirye-shiryan dawowa Harkar film

Shahararriyar jarumar Kannywood Zainab Abdullahi wacca aka fi sani da Zainab Indomie
na shirin dawo da sunanta a masana’antar.


An daina jin duriyar Indomie a masana’antar na tsawon wani lokaci bisa ga wasu dalilai.
Ubangidanta Adam Zango ne ya sanar da dawowar jarumar a shafinsa na Instagram.


Ya wallafa hotunanta saboda nuna farin cikin sa bisa biyayar da take nuna masa.
Jarumar tana daya daga cikin jarumai mata dake kan gaba a  kamfanin White house family wanda Adam Zango ke jagoranta.


Zainab Indomie tana daya daga fitattun matan kannywood da suka raya masana'antar gabanin fitowar sabbin fuskoki da ake damawa dasu yanzu.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: