Rahama mai shekaru 23 ta dauki hoton ne cikin Salo da kuma kwarewa ta daukar hoton,
Idan za’a iya tunawa a shekarar data gabata ne dai hukumar yan wasan Hausa ta dakatar da Rahama Sadau daga shirya fina finai,
sakamakon wani bidiyon waka data fito a ciki na wani mawaki Classiq, inda hukumar tayi zargin anyi rungume rungume a cikin bidiyon.
Sai dai duk da wannan dakatarwa da aka yi ma Rahama, bata yi kasa a gwiwa ba, ta yadda hukuncin ya zame mata tamkar gobarar titi a Jos,
sakamakon gayyata data samu zuwa kasar Amurka daga fitaccen mawakin nan Akon.
0 comments: