Sunday, 29 July 2018

Ni bazawara ce mai 'ya'ya 2 amma ba na so a sani - Inji Jaruma Teema Yola




Fitacciyar jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood wadda ta dade tana bayar da gudummuwar ta a masana'antar mai suna

Fatima Isa Muhammad Yola wadda aka fi sani da Teema Yola ta bayyana cewa tabbas ta taba aure har ma tana da 'ya'ya biyu, a yanzu haka amma bata so tana ya-yata hakan saboda yanayin sana'ar ta.


Jarumar ta bayyana hakan ne a yayin da take yin fira da majiyar mu ta jaridar Blueprint inda take yin karin haske a game da rayuwar ta a baya da kuma yanzu.


Teema Yola ta bayyana babban dalilin da yasa bata son tana yayata zawarcin nata, saboda kada ta kori wasu mazan dake son ta da aure.


Haka zalika jarumar ta bayyana cewa a kowane lokaci idan dai har ta samu namijin da take so zata yi auren ta domin a cewar ta cikar mace kenan a dakin mijin ta.

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: