Tuesday, 10 July 2018

Hannun wani mutumi ya makale a jikin Qur'ani.

Ikon Allah baya karewa, kamar yadda hoton wani mutumi ya karade yanar gizo, a cewar rahotanni Hannun wani mutumi ya makale a jikin Qur’ani bayan yayi yunkurin yin batanci ga Qur’anin.


Wani mai amfani da shafin zumunta na Facebook mai suna Brendan Ortono ya yi da’awar cewa yana gurin da abun al’ajabin ya faru, ya cewa.


 “Babu shakka, ina gurin, na tabbatar da hakan, munyi duk kokarin da zamuyi don muga mun cire Qur’anin daga hannun nasa amma duk kokarinmu a banza, domin mun kasa raba hannun nasa da Qur'anin. Ko yanzu da nake Magana da ku a yanzu, hannuwansa na nan makale da Qur’anin.

Ortono Brenden ya ce mutumin ya fara gudanar da mummunan kudirin nasa ne daga gida inda ya zana tambarin Cross a jikin Qur'ani, wanda kafin ya kai ga aikata ragowar rubutun da ya yi niyya, kawai sai ya ji hannunsa ya makale, kamar yadda yake shaidawa mutanen da suka taru a wajen.

Mutumin da hannuna sa ya makale a jikin Qur'ani lokacin da yake shirin batanci ga Qura'anin
Duk da haka, har zuwa yanzu ba’a tabbatar da yankin kasar da abun ya faru a ciki ba.

Muna Rokon Allah ya kara Tsare Addininmu daga sharrin Makiyya
Amen

SHARE THIS

Author:

Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...

0 comments: