- Labari mai dadi ga 'yan Najeriya, domin sun samu jika
- 'Yar gidan shugaban kasa Buhari ta haihu a kasar Andalusia ta Spain
Kimanin watanni goma sha takwas da bikin yar gidan shugaban kasa Muhammad Buhari wato Zahra Buhari, wani rahoto da ya riske mu yanzu daga kafar sadarwa ta yanar gizo ta kikiotolu.com, ya bayyana cewa 'yar shugaban kasar ta haifi santalelen jaririnta cikin koshin Lafiya, a wani asibiti da ke kasar Spain.
Wata Majiya daga zuri'arta, sun bayyana yadda wannan haihuwa ya sanya farin ciki a tsakaninsu.
Idan za'ai iya tunawa dai a cikin Shekarar 2016 ne, Zahra Buhari ta auri Ahmed Indimi dan gidan babban attajiri nan Alh. Mohammed Indimi.
Wednesday, 11 July 2018
Author: Adamu umar
Shafin Arewarmu.com shafine Dake Kawo Muku Fittatun Bayanai Akan Labaran Duniya, Labaran Gida, Hanyoyin Kiwon Lafiya, Fatawar Addinin Musulunci, Labarai Daga Kannywood, Labaran Garkuwar Jiki, Wakokin Hausa, Tafsiran Addinin Musulunci...
0 comments: